Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jonathan Ya Ja Kunnuwan Masu Neman Haddasa Rikici da Kiyayya


Shugaba Jonathan
Shugaba Jonathan

Shugaban Najeriya Jonathan mai barin gado yayi bayani da kakkausan lafazi akan wasu da yace suna neman tada zaune tsaye da yada kiyayya tsakanin alummar Najeriya.

A jawabin da mai magana da yawun fadar shugaban kasa yayi Dr Reuben Abatti da ya karantawa manema labaru a madadin shugaban kasa, shugaban yayi tur da allawadai da kalamun wasu masu fada a ji da suka yi wadanda ke neman harzuka jama'a da yiwa zaman lafiya barazana.

Yace irin wadannan mutanen suna neman cimma muradun kansu ne da na siyasa. Yace gwamnati zata dauki duk matakin da ya kamata domin ta kare hakoki da ikon da 'yan Najeriya ke dashi su zabi wanda suke so cikin lumana da zaman lafiya a zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi.

Yace shugaban kasa yayi tur da muguwar aniyar wasu 'yan siyasa ko kungiyoyi da wasu mutane dake yiwa wasu barazana. Su na kokarin tada hayaniya domin tsorata jama'a jim kadan bayan an samu sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayyar kasar.

Yace ire-iren wadannan baragurbi da kalamun batancinsu ba zasu karkata shirye-shiryen da gwamnati ke yi ba na tabbatar da an gudanar da zabe mai adalci cikin lumana da zai kara girka dimokradiya mai dorewa da 'yan Najeriya ke bukata a kasar.

Jawabin na shugaban kasa ya zo ne daidai lokacin da ake cecekuce bisa ga kalamun da sarkin Legas ya yayi yayinda 'yan kabilar Ibo suka kai masa ziyara. Sarkin yace duk wanda bai zabi dan takarar gwamna na APC ba wato Akinwumi Ambode zai tsine masa ya fada cikin teku. Kodayake sarkin ya musanta zargin amma jam'iyyar PDP tayi tur da kalamun. Ita ma APC ta nisanta kanta da kalamun.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG