INEC na karin bayani ne kan shigar da karar dakataccen kwamishinan ta jihar Adamawa, Barista Hudu Ari kara a babbar kotun jihar Adamawa.
"Mu na bukatar hukuma ce da kotu ta musamman da za ta rika daukar matakin kamawa da hukunta masu aikata laifukan zabe da su ka hada da saya da sayar da kuri'u" Inji kwamshinan labaru na hukumar Festus Okoye da ke ba da tabbacin matakan ba sani ba sabo da hukumar ke dauka ga jami'an ta da su ka karya dokokin zabe.
Okoye ya ci gaba da cewa wasu sun dauka in sun karya dokar ta hanyoyin su na zamba cikin aminci, to sun sha ba hukunci don haka ya ke da amfani a dau matakan wargaza irin wannan dabi'a.
INEC ta ce za ta gurfanar da Ari bisa tuhume-tuhume shida daga rahoton da ta karba daga rundunar 'yan sanda, kuma ka'idar ta nuna a jihar da jami'i ya aikata laifin ne za a gudanar da shari'ar sa.
Jami'a a sashen labaru ta hukumar Zainab Aminu ta yi karin bayanin yanda dokar ta ke bisa tanadin sabuwar dokar zabe.
A Laraba mai zuwa za a fara sauraron karar a Adamawa, inda har yanzu dakataccen kwamishinan ke cewa sam bai aikata wani laifi ba.
In za a tuna Hudu Ari ya aiyana 'yar takarar APC Aisha Dahiru Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan Adamawa gabanin kammala tattara kuri'u, amma daga bisani jami'in aiyana sakamakon ya kammala aikin, inda gwamna Umar Fintiri ya samu tazarce; ya na mai nuna takaicin yanda da kyar ya tsallake rijiya da baya a dambarwar aiyana sakamakon.
Za a zuba ido kan shari'ar da zuwa yanzu Ari ke matsayin wanda a ke tuhuma kuma har yanzu ya na zaman dakatarwa daga aiki ne ba sallama ba.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5