Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kararrakin Zabe Ta Najeriya Ta Fara Sauraren Sakamakon Zaben Shugaban Kasa


Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasar Najeriya PEPC
Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasar Najeriya PEPC

A yau 8 ga watan Mayu ne kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasar Najeriya za ta fara sauraren kararrakin da ke kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, wanda hukumar zabe ta INEC ta ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben.

Biyu daga cikin ‘yan takarar, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour sun yi watsi da sakamakon inda suka shigar da kara daban-daban a gaban kotun.

Atiku ya yi zargin cewa INEC ba ta aika tare da shigar da sakamakon dubban rumfunan zaben yadda ya kamata ba. A kan haka ya yi kira da a soke zaben kuma a sake gudanar da wani sabon zabe.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa tun a ranar 1 ga watan Maris, lokacin da aka ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben, ba'a aika dukkannin sakamakon zaben da bayanai da ke nuna sahihancinsu ba, wanda ya hada da tantancewa daga rumfunan zabe zuwa ga rumbun bayanai (Saver) na INEC.

Atiku ya kuma ba da misali da tashe-tashen hankula da dama, da tsoratar da masu kada kuri’a da sace akwatunan zabe, da wasu kura-kurai da suka faru a lokacin zaben.

A daya bangaren kuma, Peter Obi ya yi korafin cewa an sami kura-kurai da dama a zaben da suka hada da hana masu zabe kada kuri’a, sayen kuri’u, da kuma zargin rashin cancantar Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima, don tsayawa takarar zaben.

Obi ya kuma yi ikirarin cewa Tinubu ya gaza samun rinjayen kuri’u da kuma kashi daya bisa hudu da aka jefa a babban birnin tarayya Abuja, wanda hakan na daga cikin sharudan lashe zaben shugaban kasar. Bugu da kari, ya yi zargin cewa an gudanar da zaben ne ba tare da bin tanadin doka ba.

Hukumar ta PEPC tana da muhimmin aiki a gaban ta na duba shaidun da masu shigar da kara suka gabatar da kuma yanke hukunci kan ingancin da'awarsu.

Hukuncin kotun dai zai yi matukar tasiri ga makomar siyasar Najeriya, domin za ta tabbatar sahihancin ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben ko kuma akasin haka.

Ana sa ran za'a shafe makwanni da dama ana sauraren karar, kuma ‘yan Najeriya da sauran kasashen duniya ne ke dakon hukuncin kotun.

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa al’ummar kasar cewa za'a gudanar da zaman bisa gaskiya da adalci, ta kuma yi kira ga dukkan bangarorin da su mutunta doka da tsarin shari’a.

Gwamnatin ta kuma bukaci ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu su kuma sa hakuri, yayin da ake ci gaba da sauraren karar tare da kaucewa duk wani abu ko kalamai da ka iya tada tarzoma ko kawo cikas ga zaman lafiyar kasar.

XS
SM
MD
LG