Muryar Amurka ta zanta da sabon babban daraktan hulda da jama'a na rundunar sojojin Najeriya Kanar S.K.Usman akan sabon harin da kungiyar Boko Haram aka ce ta kai yau a garin Buni Yadi dake jihar Yoben Najeriya.
Kodayake Kanar S. K. Usman wanda abokin aiki Bello Galadanchi ya zanta dashi ya tabbatar da cewa lallai 'yan kungiyar sun kai hari amma yace bashi da wani karin bayani da zai bayar yayinda suke zantawa tare. Yace an koresu amma nan gaba sojoji zasu bayarda cikakken bayani kan lamarin.
Dangane da yakin da sojojin ke yi da 'yan Boko Haram Kanar Usman yace har yanzu suna fama da yaki dasu 'yan ta'adan. Nufin shi ne nan ba da dadewa ba so ake a ga bayansu gaba daya a kawo karshen yakin.
Yanzu dai babu wani waje da za'a ce akwai tarin 'yan ta'adan kamar da can a dajin Sambisa. Wadanda suke kai hari yanzu nan da can Kanar Usman ya ce "'yan barbashinsu" ne. Saboda haka ya gargadi jama'a da a sa ido domin dakile harin jefi jefi da yanzu suke yi.
Yace a da can sun kama kananan hukumomi da dama har ma suka kafa tasu daular amma duk wadannan an kawar dasu, an turasu sun koma dajin Sambisa. Yace wuri ya kure masu.
Akan daukan lokaci wajen samun galaba akan 'yan ta'adan cikin dajin Sambisa Kanar Usman yace akwai wasu dalilai. Na farko yanzu an shiga damina. Na biyu Sambisa ba karamin wuri ba ne. Na uku har yanzu suna rike da mutanen da suka sata saboda haka ana gudun kada a rutsa da rayukan mutanen. Yace ana bakin kokari a tabbatar an yi maganinsu.
Kanar Usman ya mayar da martani akan labarin da wasu suke yayatawa cewa akwai alamar za'a tattauna da kungiyar domin sako 'yan matan Chibok 219 da har yanzu kungiyar ke garkuwa dasu. Yace Allah ya sa hakan ya faru.
Ga firar Bello Galadanchi da Kanar S. K.Usman.
Your browser doesn’t support HTML5