Kungiyar IZALA ta kirawo taron manema labarai inda ta yi Allah wadai game da sabbn hare-haren da aka kai Jos a jihar Filato da Potiskum a jihar Yobe jiya Lahadi.
Hare- haren sun yi sanadiyar asarar rayuka masu yawa. Yayin da na Potiskum mutane takwas suka mutu na Jos ya lakume rayuka arba'in da hudu.
Kungiyar IZALA ta bakin shugabanta na kasa Abdullahi Bala Lau ta yi zargin cewa hare-haren nada wasu manufa saboda haka, tace dole ne gwamnatin kasar ta tashi tsaye kana al'ummar kasa su bada hadin kai.
Yace an auna hari kan shugabanninsu da malamansu domin a ga cewa an far masu cikin azumin Ramadan.Yace abu ne na bakin ciki kuma fatar ita ce Allah ya tona asirin duk wadanda suke da hannu ciki.Gwamnati ta gano wadanda suke da hannu a ciki. Yace shin me suke nufi ? Sun kashe musulmi sun kashe wanda ba musulmi ba to menene abun nufi?
Malam Danladi Musa wani masani a harkokin tsaro ya bayyana yadda za'a gane dan kunar bakin wake. Ga wasu daga cikin alamun gane 'yan kunar bakin wake kamar yadda Danladi Musa ya bayyana.
1. 'Yan Boko Haram nada dabi'ar barin gemu a yamutse.
2. Idan zasu kai harin kunar bakin wake suna aske jemun.
3. Idan zasu kai hari inda suka shirya zasu kai hari nan suka sa gaba. Basa kulawa da kowa da komi ko su dinga wani waige waige.
4. Idan suna dauke da wani abu su kan yi tafiya da sauri-sauri
5.Idan suna dauke da wani abu a jikinsu za'a a ga sun yi kiba a jiki amma ba za'a ganta a fuska ba amma rigarsa zara dan daga.
To saidai sabuwar gwamnatin Najeriya ta hakikance cewa da gaske take yi wajen kawo karshen ta'adancin Boko Haram dalili ke nan shugaban kasar ya fara ziyartar kasashen dake mkwaftaka da Najeriya musamman wadanda Boko Haram ta taba su.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.