Yau China da Wasu Kasashe Zasu Yiwa Bankin Duniya Kishiya

Wang Yang, mataimakin Fiyain Ministan China, kasar da take ta kaso mafi tsoka a sabon bakin

Yau Litinin wakilai daga kasashe 57 ne suka halara a babban dakin taro na China a Beijing domin su sanya hanu kan yarjejeniyar kafa sabon bankin da China take yiwa jagoranci wanda zai bada karfi wajen zuba jari kan harkokin sifiri da wasu sassa na ci gaba.

Australia ce kasa ta farko da ta sanya hanu kan yarjejeniyar, da aka kafa da zummar samar da kudade zunzurutu har dala milyan dubu dari takwas ko wace sheklara domin ayyukan gina hanyoyi na mota da jiragen kasa, da na ruwa, hanyoyin sadarwa, da kuma makamashi.

China zata samar da kusan dala milyan dubu 30 na jarin kafa bankin, cikin dala miliyan dubu dari da ake bukata, kuma zata mallaki kashi 25 cikin dari na iko a bankin. Kasashen India da Rasha sune na biyu dana uku a jerin mafiya hanun jari a bankin.

Wasu suna kallon wannan sabon banki , a zaman kishiyar Bankin duniya da bankin raya yankin Asiya. Amurka da Japan sunki shiga bisa dalilan cewa suna fargabar za'a gudanar da harkokin bankin cikin duhu, da kuma rashin adalci, da kuma gudun bankin ba zai mutunta muhalli da kuma dokokin kwadago ba.

Amurka ta gaza hana kawayenta masu yawa ciki harda kasashen Afirka da turai da kasashe da suke Amurka ta kudu zama wakilai a bankin.