An dai samu nasarar ceto mutane 14 tun bayan da jirgin mai suna Eastern Star ya nutse a farkon makon nan saboda matsanancin yanayi mara kyau.
Hukumomin kasar sun ce zai yi wuya sauran mutanen da suka rage su kasance a raye, kamar yadda wannan jami’in watsa labaran yankin Hu Kaihong ya tabbatar.
“Ya zuwa karfe 12 na ranar yau 6 ga watan Yuni, daga cikin mutane 456 da ke cikin jirgin, mutane 14 kawai aka ceto, kuma adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya kai 396, har yanzu ba a ga mutane 46 ba.” Inji Kaihong
Matsananciyar guguwa hade da ruwan sama da igiyar ruwa mai karfi, sun kara dagula ayyukan ceton a cewar jami'in.
Yanzu haka iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, suna kalubalantar hukumomi, cewa bai kamata jirgin ya yi wannan tafiya ba, bisa la’akkari da cewa an yiwa matukansa gargadin cewa babu yanayi mai kyau.