Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Girka zata yi kuri'a raba gardama.


Wani dan kasar Girka yace yin zanga zanga
Wani dan kasar Girka yace yin zanga zanga

Ministocin kudi kasashen turai suna yin wani taron gaggawa yau Asabar, bayan da kasar Girka tace zata sa ayi zaben jin ra'ayi ko kuma na raba gardama akan sakamakon tattaunawar da aka yi na bada bashin ceton kasar.

Ministocin kudi kasashen turai suna yin wani taron gaggawa yau Asabar, bayan da kasar Girka tace zata sa ayi zaben jin ra'ayi ko kuma na raba gardama akan sakamakon tattaunawar da aka yi na bada bashin ceton kasar.
A yayinda yake zantawa da 'yan jarida kafin taron a birnin Brussels kasar Belgium, shugaban Eurozone yace shawarar da Girka ta yanke bai dace ba.
Shima Ministan harkokin wajen Jamus furucin makamancin na shugaban Eurozone. Yace bisa fahimtar sa gwamnatin Girka ita ta kawo karshe tattaunawar da ake yi.
Prime Minitan Girka Alexis Tsipiras ya samu kyakyawar tarbo a Majalisar dokokin Girka a yau Asabar, wadda ke zama domin tattauna bukatar gwamnati na yin kuri'a jin ra'ayi. Wani lokaci a yau Asabar ake sa ran Majalisar zata jefa kuri'a akan wannan batu.
Jiya Juma Mr. Tsipiras ya bada wannan sanarwa a wani jawabi daya gabatar da gidan talibijin na kasar. Yace tilas yan kasar sune zasu yanke hukunci a zaben jin ra'ayin da za'a yi ba tare da ci da ceto ba. Prime Minista yace a ranar biyar ga watan Yuli idan Allah ya kaimu za'a jefa kuri'ar raba gardamar.
Prime Ministan yayi wannan kiran ne sa'o'i bayan da shawarwari na baya bayan nan da masu bada bashi na kasashen turai da Asusun IMF suka kasa cimma yarjejeniya.
Kasar Girka tana bukatar bashin dala biliyan takwas na kudin ceton tattalin arziki daga kungiyar kasashen turai, domin ta samu zarafin biyan kusan dala biliyan biyu ga Asusun IMF kafin ranar Talata mai zuwa/

XS
SM
MD
LG