Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Yi Fatali Da Sukan Amurka


Shugaban kasar China Xi Jingping
Shugaban kasar China Xi Jingping

Dangantaka tsakanin Amurka da China na kara yin tsamari, inda a kwanan nan China ta yi watsi da sukar da Amurkan ke yi na mallake wasu filaye da Chinan ke yi a yankin Kudancin tekun kasar.

China ta yi fatali da sukar da Amurka ta yi mata, kan karbe filaye a yankin teku da ke kuduncin Chinan.

Wani Babban Hafsan sojin kasar ta China, Sun Jianguo, ya bayyana a wani taron koli da aka yi a Singapore cewa ayyukan gine-gine da Chinan ke yi a bisa ka’ida ne, kuma suna daga cikin abubuwan da al’umar kasashe za su amfana.

Ya kuma kara da cewa babu wani abin tuhuma a wadannan gine-gine da China ke yi, yana mai jaddada cewa Chinan ba ta canja matsayarta ba, kan matakan da ake bi na ganin an tabbatar da zaman lafiya ta hanyar tattaunawa da tuntuba.

Manyan jami’an diplomasiyya da ‘yan jarida sun yiwa Mr. Sun tambaya bayan da ya kammala jawabinsa, amma sai ya basu amsa ta hanyar karanta takardar jawabinsa, ba tare da ya fayyace musu abubuwan da suka tambaya ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG