Yau ce Ranar Matasa ta Duniya: Buhari Ya Yaba Masu

Matasa dake murnar zaben Buhari

Ko shakka babu matasan Najeriya da ma yawancin kasashen duniya matasa na taka rawar gani a harkokin zabe da cigaban kasa

Yau Laraba 12 ga watan Augusta rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe kowace shekara ta tunawa da matasa da irin taimakon da suke yi a kasashensu da ma duniya gaba daya.

Saboda haka yau a Abuja shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya yabawa matasan kasar saboda irin gagarumin gudummawar da suka bayar wanda ya taimaka wurin samun sakamakon zaben 2015.

Shugaba Buhari da yake magana a wurin bikin ranar matasa ta wannan shekarar ya yabawa matasan Najeriya saboda mahimmiyar rawar da suka taka a zaben 2015. Rawar da matasan suka taka a zaben ta sa zaben ya zamo wani misali na kwarai wajen shimfida tafarkin dimokradiya a nahiyar Afirka.

To saidai shugaban ya nuna damuwarsa saboda habakar tattalin arzikin Najeriya bai inganta rayuwar matasan kasar su kimanin miliyan sittin ba duk da cewa su ne suka fi yawa.

Shugaba Buhari yace kodayake a fannin ilimi matasa sun yi gaba cikin shekaru goma da suka gabata amma manhajan karatun da aka koyar dasu bai taimaka masu ba wurin samun irin horon da suke bukata da zai anfanesu. Yace wannan kalubale ne a kasar.

Shugaban ya tabbatarwa matasan kasarsa cewa gwamnatinsa zata tanadi ingantaccen yanayin da zai taimaka wurin habaka ma'aikatu masu zaman kansu saboda su kirkiro ayyuka da matasan zasu samu su yi.

Wakazalika shugaban yace gwamnatinsa zata taimakawa masana'antu da abubuwan da suke bukata saboda su kirkiro ma matasa ayyuka musamman yadda zasu kafa nasu ma'aikatun.

Gwamnati zata samarda kudaden da zasu hanzarta habakar masana'antun cikin gida.