Shi dai taron bunkasa tattalin arzikin Afirka za'a gudanar dashi ne a birnin Nairobi babban birnin Kenya a wannan watan.
Taron na Kenya zai samu halartar shugaban kasar Amurka Barack Obama da wasu shugabannin Afirka da 'yan kasuwa da dama.
Mahalarta taron na Abuja kimanin su dubu daya an zabosu ne daga jerin masu neman halartar taron Kenyan kimanin su dubu ashirin daga kasashen Afirka hamsin da daya.
Tuni dai gidauniyar Elumelu ta kafa wata gidauniyar samarda jari na dalar Amurka miliyan dari ko kuma sama da nera miliyan dubu ashirin domin tallafawa shirin na samarda aikin yi ga matasa domin dogaro da kai da kuma kishin Afirka..
Wani matashi daga kasar Uganda ya shaidawa Muryar Amurka alfanun taron garesu. Yace shi injiniyan sarafe-sarafe ne kuma yana fatan kafa kamfanin sarafa madarar waken soya bisa ga la'akari da ingancinsa kan lafiyar jiki. Yace fatarsa a taron shi ne samun karfin gwiwa da taimako daga manyan 'yan kasuwan Afirka.
Danjuma Muhammad Yalwa daga jihar Kebbi ya bayyana irin kwarin gwiwar da yake dashi dangane da taron. Yace taron na 'yan kasuwa ne masu tasowa da shi Tony Elumelu yake son ya taimakawa ba 'yan Najeriya kadai ba har ba kasashen Afirka gaba daya. Yace saboda haka ne ya gayyato mutane dubu daga Afirka domin karawa juna ilimi.
Horon da mahalarta taron zasu samu ya hada da bangarorin aikin noma da ilimi da dinke dinke da kuma fannin sadarwar kwamfuta.
Ga rahoton Babangida Jibrin.