Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NYSC: Gwamnatin Buhari Zata Inganta Shirin Aikin Bautawa Kasa


Matasa
Matasa

Gwamnatin Buhari zata cigaba da shirin bautawa kasa da ya samo asali lokacin shugabancin Janar Gowon amma zata inganta shi

Yau Laraba Shugaba Muhammad Buhari ya bada tabbacin cigaba da shirin nan na bautawa kasa da daliban jami'a da suka gama karatunsu ke yi na shekara daya

Shugaban yace gwamnatinsa zata dauki duk matakan da suka dace saboda inganta shirin a matsayin hanyar tabbatar da hadin kan kasa da cudanya tsakanin al'ummominta.

Shugaban ya bada tabbacin ne yayin da ya karbi rahoto daga jami'an ma'aikatar matasa da cigaba a karkashin jagorancin babbar sakatariyar ma'aikatar Mrs. Rabi Jimeta.

Shugaba Buhari ya jaddada ban gaskiyarsa ga shirin yana cewa dalilan da suka sa aka kafashi shekarar 1973 har yanzu suna da mahimmanci da cigaban kasar.

Yace ya yadda da shirin kuma yana tunanen yakamata ya cigaba saboda karfafa cudanya. Yace "duk lokacin da na je gida Daura na kan nemi masu bautawa kasa daga Legas da Aba da wasu sassan kasar".

Ya kara da cewa "Na kan yi murna idan na ji cewa sanadiyar aikin bautawa kasa ne wasu suka bar jihohinsu zuwa wasu garuruwan kasar"

Mrs Rabi Jimeta ta shaidawa shugaban kasa cewa yawan karuwar masu bautawa kasa kowace shekara na zama wani kalubale ga shirin saboda rage kudinsu da ake yi daga kasafin kudin kasa. Saboda haka basu iya kula da bukatunsu.A shekarar 1973 da aka soma shirin dalibai 2,364 ne kawai. Daga shekarar 1974 zuwa 2014 dalibai sun karu har sun kai 229,016.

Karuwar jam'o'i zai sa daliban su kai 300,000 nan da shekarar 2020.

Daraktan NYSC din Janar Johnson Olawumi ya shaidawa shugaban kasa shirin mayarda bautawa kasa na son kai saboda rage kashe kudi.

XS
SM
MD
LG