Wani likita a Asibitin Kula Da Masu Tabun Hankali da ke Maiduguri, jahar Borno ya ce da dama daga cikin ‘yan gudun hijirar da ‘yan Boko Haram su ka dugula wa rayuwa, ciki har da mata, sun runguma shaye-shaye.
Dakta Babagana Machina ya ce masu tabun hankalin sanadiyyar halin da su ka samu kansu na ta karuwa. Hasalima, in ji shi, mata sun kai kashi 15%. Y ace fiye da rabin masu tabun hankalin da ke asibitin, shan kwaya ya jawo masu.
Dakta Machina y ace banda hauka, kwayoyi na iya illa ga sauran sassan jikin mutum musamman hanta da koda da sauransu. Ya ce kodayake ana samun karuwar ‘yan kwaya cikin mata da wadanda su ka manyanta, fiye da kashi 70 na ‘yan kwayan da ke asibitin matasa ne. Y ace raba mutane da muhallansu da kuma wuraren aikinsu da ‘yan Boko Haram su ka yi ya dada haddasa shayeshaye.
Wani mazaunin birnin na Maiduguri mai suna Alhaji Abdulkarim Abbas ya ce yanzu har matan aure da jami’an tsaro, kuma ko ina ana sayarwa. To amma hukumomin tsaron sun karyata cewa jami’ansu na shan kwayoyin.
Wakilinmu a Maiduguri, Haruna Dauda ya aiko da labarin.