Da yake magana kan dalilin shirya taron shugaban taron kasa, Hon Charles Olufemi Folayo, ya gayawa wakilin Sashen Hausa Hassan Maina Kaina cewa, burin taron shine tattaunawa kan makomar matasa a Najeriya
Mr. Folayo yace sanin cewa matasa sune kashin bayan kowace al'uma, ya zama tilas a maida hankali kan muradunsu domin sune zasu kawo ci gaban tattalin arziki da habaka hanyoyin kawo ci gaban al'uma da kasa.
Wasu daga cikin masu halartar taron sun bayyana cewa suna halarci taron domin su tattauna kan bukatunsu. Kamar yadda wakiliya a majalisar matasan, Fatima Maina Abdullahi tayi bayani. Ta bayyana fatar zuwa karshen taron zasu fito da matsaya dangane bukatun matasa.
Wata wakiliya daga jihar Edo tace ta halarci taron ne da zummar karuwa kan muhimman bukatun matasa.
Ga karin bayani.