Takaddama tsakanin kokuwar shugabanci tsakanin matasan arewacin Najeriya da na kudanci a wurin babban taron kasa na matasan Najeriya ta kai ga kusan tara wa juna gajiya.
Wani wakili daga arewacin kasar mai suna Abdullahi Aliyu Katsina ya shaida ma wakilinmu Hassan Maina Kaina cewa ‘yan arewacin Najeriya sun fi ‘yan kudu mutanen da su ka dace musamman a wurin taron, to amma sai ‘yan kudun su ka nemi yin babakere duk kuwa da rashin mutane na kwarai daga kudun. Y ace hakan ya sa su ‘yan arewa su ka ce wannan karon ba zau lamunta da zaben tumun dare ba ko dauki dora ba.
A daya bangaren kuma, wani wakili daga kudu mai suna Barrister Aremu Azan, ya ce da ma kowane bangare na kare muradunsa ne a taro irin wannan. Don haka su ma matasan kudu sun shiga kare muradunsu. To amma ya ce za a yi kokarin ganin an shawo kan wannan matsalar.
Haka zalika wata gardama ta barke game da shakkar da wasu wakilan kudancin kasar su ka nuna kan ainihin shekarun wakilin jahar Yobe a wurin taron, Dauda Muhammad Gombe, wanda don haka aka gayyace shi da ya je gaban jama’a ya kare ikirarinsa na kasancewa dan shekarun da ya bayyana. Ya kuma kare kansa. Wani matashi dai y ace lallai akwai wasu da ba matasa ba ne kuma an sha ganinsu a tarurrukan da su ka gabata da sunan matasa.