A yau Laraba kasar Pakistan ta rataye mutane 4 bisa alaka da harin ‘yan Taliban a wata makaranta da Sojin kasar ke tafiyarwa a garin Peshawar a bara. Lokacin da har ‘yan ta’addar suka hallaka yara dalibai guda 134 da kashe ma’aikatan makarantar guda 16.
Sojojin sun bayyana cewa, an yankewa mutanen hukunci da kuma kashe su tare da wasu mutane guda biyu da aka samu da laifin taimakawa ‘yan bindigar da suka budewa daliban wuta.
Shedu sun bayyana yadda ‘yan bindigar suka budewa yaran wuta a lokacin da suke taron haduwar safe a makarantar a dakin da suke taruwar, daga baya kuma suka dinga bi aji-aji suna bindige duk dalibin da suka gani.
Sojojin dai a lokacin sun kashe duk ‘yan bindigar da suka yi wannan aika-aika har su 4 a ranar bayan fafatawar sa’o’i 4 tsakanin su ana musayar wuta. ‘Yan Taliban dai sun ce harin daukar fansa ne ga kasar game da sanya sojojinta farautarsu.
Firaministan Pakistan Nawaz Sharif ya yi magana kan janye dakatar da hukuncin kisan da kasar tayi wanda da yake tun a shekarar 2008. Kama zuwa yanzu sun kashe daruruwan mutane.