Masu bincike a Indonesia sun ce, wata tangardar na’ura ce ta sa matuka jirgin kasar suka dauki wani mataki da ya haddasa faduwar jirgin saman fasinja a cikin teku a watan Dismabar bara.
A wani rahoto na karshe da ta fitar, Ma’aikatar kiyaye hadurran ababan hawa a kasar, ta ce na’urar kula da tafiyar jirgin samfarin Airbus A 320 ce ta samu lahani, wanda hakan ya yi sanadiyar hadarin.
Rahoton ya kuma nuna cewa matakin da matukan jirgin suka dauka, bayan da na’urar ta samu matsala ne, ya sa suka kasa daidai tafiyar jirgin, lamarin da ya sa jirgin ya gagari iyawarsu.
Wani rahoto na baya, ya nuna cewa bayan haka, jirgin ya rikito kasa sannan daga baya ya tsunduma cikin ruwa.
Duk dai mutane 162 da ke cikin jirgin suka halaka.