Yayin da ya ke ba da bahasi a gaban kwamitin Majalisar kasar da ke kula da rundunar sojin Amurka a jiya Talata, Carter ya ce, dakarun za su taimakawa takwarorinsu na Iraqi da kuma na Kurdawan Pershmerga a yakin da suke yi da IS.
A cewar Carter, gwamnatin Iraqi na sane da wannan shirin aikewa da dakarun.
Sai dai Sakataren Tsaron na Amurka bai ambaci adadin dakarun da za a tura ba, amma ya ce suna da matukar yawa kuma sun haura wadanda aka tura zuwa Syria.
A watan Oktoba shugaba Barack Obama ya tura da dakarun kasar sama da 50 zuwa Syria domin kai dauki na musamman ta hanyar tsara aikace-aikacen mayakan sa kai na cikin gida, da na dakarun kawance da Amurkan ke jagoranta.
Carter ya kara da cewa, dakarun suna shirin fara aiki a Syrian ba tare da ya fadada bayaninsa kan takamaimai yaushe za su fara ba.
Daga cikin ayyukan da dakarun za su gudanar, akwai kwato mutanen da ake garkuwa su da su, da kai hare-hare da tattara bayanan sirri da kuma kama shugabannin kungiyar ta IS.