Ma’aikatar tsaron kasar tace sojojin nasu sun bibbindige ‘yan ta’addar suka kuma saki mutanen da suka kama din a lokacin wani samamen da suka kai musu a makon da ya gabata a tsakanin kan iyakar Kamaru da Najeriya.
Sai dai har yanzu ba wani kwakkwaran tabbacin wannan ikirari nasu. Hukumomin kasar ta Kamaru na zargin ‘yan boko haram da kai harin da ya hallaka jama’a a Arewacin kasar a makon da ya shude.
‘Yan kunar bakin wake ne suka tada kansu a wani gari Waza kusa da kan iyakar Najeriya da kasar. Kamaru dai na ta fama da yaki da ‘yan boko haram akan iyakokin tun daga shekarar 2013.
‘Yan boko haram sun hallaka sama da mutane 10,000 a jihohin Musulmin jihohin kamar shida na Arewacin Najeriya cikin shekaru 6 da suka wuce.