Wannan sanarwar ta fito a taron da kasashen duniya ke yi a birnin Paris kan sauyin yanayi, inda ake yunkurin a aga an rage ababan da ke haifar da illa ga yanayi da kashi 50, da kuma rage dogaro da ruwa da kashi 80, domin samar da tsabtacciyar hanyar samar da wutar lantarki da kashi 100.
Haka zalika, a jiya Talata shugaban Faransa, Francois Hollande, ya bayyana cewa kasarsa za ta baiwa Afrika tallafin dala biliyan 2.1 nan da shekaru hudu masu zuwa, domin su inganta hanyoyin samar da wutar lantarki ba tare da sun dogara da yin amfani da mai ba.
Shugaban Barack Obama, har ila yau ya gana da wasu kananan kasashen da ke kan tsibirai, kan yadda sauyin yanayi ke shafarsu.
Daya yawa daga cikin kasashen da ke halartar wannan taro, sun amince da daukan matakan samar da kariya ga dazuka.
Baya ga haka, Brazil da Norway, sun ayyana cewa za su karfafa dangatakarsu domin kare dazukan da ke tsakaninsu, yayin da Burtaniya da Jamus da Norway suma suka ce za su samar da dala biliyan daya a duk shekara na tsawon wa’adin shekaru biyar, ga kasashe, domin su rungumi matakan rage kaifin illar sauyin yanayi kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tsara.