'Yan Tawayen M23 Sun Kwace Wani Muhimmin Gari A Congo

‘Yan Tawayen M23 - Congo

Wata kungiyar 'yan tawaye da ake zargin tana da alaka da kasar Rwanda ta kwace garin Rubaya da ke gabashin kasar Congo inda ake hakar ma'adanai a gabashin kasar da ya shahara wajen samar da wani muhimmin ma'adinan da ake amfani da su a wayoyin salula na zamani, a cewar kungiyar a ranar Alhamis.

WASHINGTON, D. C. - A cikin wata sanarwa da aka raba da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press, mai magana da yawun kungiyar 'yan tawayen M23 ya shaida cewa an kwato garin.

Amma sojojin Congo sun ki cewa komai kan lamarin.

Congo

Rikicin da aka kwashe shekaru da dama ana yi a gabashin Congo ya haifar da daya daga cikin mafi munin matsalar tagayyar jama’a a duniya, inda sama da kungiyoyi 100 masu dauke da makamai ke fafatawa a yankin mai arzikin ma'adinai kusa da kan iyaka da Rwanda.

Ana zargin kungiyoyi da dama da aiwatar da kashe-kashen jama'a da fyade da sauran laifukan cin zarafin bil'adama.

Rikicin dai ya raba kimanin mutum miliyan 7 da gidajensu, inda da dama ba a iya samun kai musu agaji ba.

Garin Rubaya yana da tarin ma’adinin Tantalum, wanda ake cire shi daga Coltan, wani muhimmin bangaren abun kera wayoyin hannu.

Yana daga cikin ma'adinan da aka ambata a farkon wannan watan a cikin wata wasika daga gwamnatin Congo tana yi wa Apple tambayoyi game da sanin ko kamfanin na fasaha na da labarin "ma'adinan jini" wato da ake safarar su a cikin wadanda ake sayar musu.

"Faɗuwar garin Rubaya wata hanya ce da za ta haifar da babbar ɓarna," in ji Ernest Singoma, wani ɗan fafutukar farar hula a Goma, ya shaida wa AP ranar Alhamis.

An yi ta samun tashin hankali a cikin 'yan watannin nan tsakanin 'yan tawayen M23 da sojojin Congo, kuma hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke shirin janye dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin nan da karshen shekara.

Shugaban kasar Congo Felix Tshisekedi

Shugaban kasar Congo Felix Tshisekedi ya yi zargin cewa Rwanda na ta da zaune tsaye a Congo ta hanyar mara wa 'yan tawayen M23 baya.

Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya, tare da ma'aikatar harkokin wajen Amurka, sun kuma zargi Rwanda da marawa 'yan tawaye baya, zargin da Rwandan take musantawa