Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takun Saka Tsakanin Kasashen Rwanda Da Dimokaradiyar Jamhuriyar Congo Na Kara Zafafa.


Kinshasa tana zargin Kigali da taimakawa ayyukan kungiyar ‘yan tawaye M23 a gabashin DR Congo, yayin da ita Rwandan ke zargin Congo da taimakawa ayyukan kungiyar ‘yan tawayenta ta Democratic Forces for Liberations of Rwanda FDLR.

Nunawa juna yatsun na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zabuka a DR Congo a ranar 20 ga watan Disamba da kuma karuwan fadace fadace a yankin gabashin kasar.


A wannan mako dan takarar shugaban kasa a DR Congo, Neol Tshiani ya fadawa Muryar Amurka a ranar Litinin cewa zai kaiwa Rwanda hari idan aka zabe shi.


A hirar ta da James Butty na Muryar Amurka, kakakin gwamnatin Rwanda Yolanda Makolo ta fada cewa, abin takaici ne ‘yan siyasar DR Congo suna kokarin huce takaici akanta a matsayin dabarun siyasa, kuma "ya bayyana karara cewa suna hakan ne saboda gazawarsu wurin mulkin kasar su da kuma samar da ci gaba ga jama’ar su."


Da aka tambaye ta da gaske ne gwamnatin Kigali tana taimakawa kungiyar M23, sai Makolo ta ce "Jamhuriyar dimokaradiyar Congo ta sanya dokokin ta baci a kananan hukumomi da dama a gabashin kasar a farkon shekarar 2021, saboda babbar matsalar tsaro a wurin, tun ma kafin sake bayyanar kungiyar ta ‘yan tawayen M23."

To sai dai ana ci gaba da tattaunawa a Sadec domin aikewa da tawaga zuwa DR Congo saboda rashin zaman lafiya a wannan yanki, ko Rwanda za ta taimaka ma wannan aiki? Kakakin ta bayyana cewa,

"Na tabbatar akwai akalla yunkuri biyu da ake yi domin warware tashin hankali a gabashin DR Congo, wanda kungiyar kasashen Afrika ta Gabas, da Kungiyar tarayyar Afrika suke jagoranta da kasashen duniya suke goyon baya. Yana da muhimmanci a tsara irin wadannan ayyukan zaman lafiya, amma abu mafi muhimmanci kuma shi ne ikon aiwatarwa a siyasance daga gwamnatin DRC a kan abinda aka amince, sai dai akwai alamar ko sun saba ko kuma sun gaza aiwatar da abin da aka cimma."


An samu tashin jijiyoyin wuya a Majalisar dokokin kungiyar kasashen Afrika ta Gabas yayin da sabuwar mamba DRC ta zargi Rwanda da shirya tashin hankali da kuma taimakawa kungiyar ‘yan tawayen kasar. Hakan na zuwa ne yayin da arangama tsakanin sojojin DR Congo da mayakan ‘yan tawayen M23 ke karuwa a cikin wannan wata.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG