Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Tawayen M23 Ba Su Janye Ba – Shugaban D.R. Congo


'YAN TAWAYEN KUNGIYAR M23 / Goma DRC Congo
'YAN TAWAYEN KUNGIYAR M23 / Goma DRC Congo

Shugaban kasar Congo Felix Tshisekedi ya fada a ranar Talata cewa, kungiyar ‘yan tawayen M23 ba ta kammala ficewa gaba daya daga yankunan da ta kwace a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ba, yana mai zargin mayakan da yin karya ga yarjejeniyar da aka cimma da su ta janye sojojinta.

Shugabannin yankin sun kulla wata yarjejeniya a cikin watan Nuwamban bara, wanda a karkashinta kungiyar da Tutsi ke jagoranta ta amince ta fice daga wuraren da ta kwace kwanan nan ya zuwa ranar 15 ga watan Janairu, a wani bangare na kokarin kawo karshen rikicin da ya raba akalla mutane 450,000 da muhallansu tare da haddasa rikicin diflomasiyya tsakanin Congo da makwabciyarta Rwanda.

“Duk da matsin lamba daga kasashen duniya, kungiyar tana nan a wurin,” In ji Tshisekedi yayin wani taron Hukumar Tattalin Arziki ta Duniya a Davos, a kasar Switzerland.

Ya ce “Suna yaudara kamar sun fita, suna nuna kamar suna ficewa, amma ba haka ba ne. Kawai suna zagayawa ne, suna sake koma wasu wuraren, suna zama a garuruwan da suka kama.”

Kalaman nasa dai shi ne karon farko da hukumomin kasar Congo suka fito karara kan yadda suke kallon aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya.

FILE - Shugaban Kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Felix Tshisekedi
FILE - Shugaban Kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Felix Tshisekedi

“Shugaba Tshisekedi wannan kawai zai iya fada. Gwamnati ce ba ta mutunta yarjejeniyar tsagita bude wuta ba, tana kuma ci gaba da taimakawa kungiyoyin da ke dauke da makamai,” in ji Lawrence Kanyaka, kakakin kungiyar M23.

A farko watan Janairu, wani rahoton sirri na cikin gida na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ba zai yiwu a tabbatar da janyewar kungiyar ta M23 daga wasu yankuna ba, saboda ci gaba da ayyukan dakarun, kuma binciken ya nuna cewa kungiyar ta kwace wani sabon yanki a wasu wurare.

Tshisekedi ya sake zargin Rwanda da rura wutar rikicin ta hanyar marawa ‘yan tawayen baya, zargin da wasu kasashen yammacin duniya da kwararrun Majalisar Dinkin Duniya suka yi. Rwanda dai ta musanta hakan.

Kungiyoyin fararen hula da dama ne suka yi kira da a gudanar da zanga zanga a ranar Laraba a babban birnin lardin Goma, domin nuna adawa da jinkirin da aka samu wajen aiwatar da janyewar kungiyar ta M23, duk da cewa mahukunta birnin ba su ba da izinin gudanar da tattakin ba.

Reuters

XS
SM
MD
LG