Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga-zanga A Congo Sun Kona Tutocin Amurka Da Belgium Kusa Da Ofishin MDD


Kinshasa, Congo
Kinshasa, Congo

'Yan sanda a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango sun harba barkonon tsohuwa a ranar Litinin don tarwatsa masu zanga-zangar da suka kona tayoyi da tutocin Amurka da na Belgium a kusa da ofisoshin jakadancin kasashen Yamma da na MDD a birnin Kinshasa don nuna fushinsu kan rashin tsaro a gabashin kasar.

WASHINGTON, D. C. - Masu zanga-zangar da suka yi amfani da wata sabuwar dabara ta kai hari kan ofisoshin jakadanci, sun ce kasashen Yamma suna goyon bayan makwabciyarta Rwanda, wadda ake zargi da marawa 'yan tawayen M23 da Tutsi ke jagoranta, wadda ci gabanta ke barazana ga birnin Goma mai mahimmanci a gabashin kasar.

Congo
Congo

Rwanda dai ta musanta zargin, Kongo, gwamnatocin kasashen yammacin duniya da suka hada da Amurka da Belgium, da kuma wata kungiyar kwararru ta Majalisar Dinkin Duniya sun ce kungiyar 'yan tawayen na cin gajiyar tallafin da Rwanda ke bayarwa.

Duk da cewa an tsaurara matakan tsaro bayan harin da aka kaiwa jami'an Majalisar Dinkin Duniya da motoci a ranar Asabar, gungun masu zanga-zangar sun taru a ofisoshin jakadancin Amurka da Faransa da kuma ofisoshin tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Congo da aka fi sani da MONUSCO.

Kinshasa, Congo.
Kinshasa, Congo.

Wasu sun yi jifa da duwatsu, inda suka yi yunkurin karya kyamarorin sa ido a daya daga cikin ofisoshin jakadancin Amurka, yayin da wasu kuma suka rika rera waka waka suna cewa "Ku bar kasarmu, ba ma son munafurncinku."

Pepin Mbndu, daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce "Al'ummar Yamma ne ke da hannu a sace-sacen da ake yi a kasarmu, Rwanda ba ta aiki ita kadai, don haka dole ne su bar kasarmu."

Kinshasa, Congo
Kinshasa, Congo

'Yan kallo sun yi ta murna yayin da wani mai zanga-zangar ya cire tutar Tarayyar Turai, EU daga kofar wani babban otel da ke tsakiyar birnin Kinshasa, a cewar faifan bidiyo da aka yada a kan dandalin X wadda a da aka fi sani da Twitter. Amma kamfanin dillancin labarai ta Reuters bai tabbatar da wannan faifan bidiyon ba.

Fabrice Malumba, wani direban babur da ke halartar zanga-zangar da aka yi a gaban ofishin jakadancin Amurka, ya ce "Al'ummar kasa da kasa sun yi shiru yayin da ake kashe 'yan Kwango, suna ba da kudin wa Rwanda." 'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa tare da fatattakar masu zanga-zangar.

Congo, Feb. 12, 2024.
Congo, Feb. 12, 2024.

Mataimakin Firai Ministan kasar Congo kuma Ministan Harkokin wajen kasar Christophe Lutundula ya gana da jakadu da shugabannin ofisoshin diflomasiyya a birnin Kinshasa a jiya Lahadi. Ya ce za a dauki matakan tsaro domin kare wakilcin su.

Shugaban 'yan sandan Kinshasa Janar Blaise Mbula Kilimba Limba ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, "Kamar yadda kuke gani, muna tabbatar da tsaron ofisoshin jakadanci na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango bisa yarjejeniyar Vienna."

Kinshasa, Congo
Kinshasa, Congo

Shekaru goma da aka kwashe ana tashe-tashen hankula a gabashin Kongo tsakanin dubunnan kungiyoyi masu dauke da makamai a kan filaye da albarkatu da kuma munanan hare-hare kan fararen hula sun kashe dubban daruruwan mutane tare da raba wasu sama da miliyan 7 da muhallansu.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG