Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Uku Sun Mutu Sakamakon Harin Bam A Wani Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Congo


Congo
Congo

Wasu gungun 'yan tawaye sun kai harin bam a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke lardin Kivu ta Arewa da ke gabashin Congo inda suka kashe fararen hula uku tare da jikkata wasu takwas, a cewar wata kungiyar fararen hula a jiya Talata.

WASHINGTON, D. C. - Hakan na zuwa ne yayin da tashe-tashen hankula a yankin da ke fama da rikici ya haifar da zanga-zanga, kuma kungiyar agaji ta yi gargadin cewa dubban mutane na fuskantar rashin samun damar taimako.

Congo
Congo

Wata kungiyar ‘yan tawaye da ake zargin tana da alaka da makwabciyarta Rwanda, ta kai harin bam ranar Talata a sansanin Zaina mai tazarar mil 16 daga birnin Goma, in ji shugaban kungiyoyin fararen hula, Wete Mwami Yenga. Harin bam din ya biyo bayan hare-haren da aka kai kwanaki kadan daga wannan birnin.

Kungiyar 'yan tawayen na M23 dai ba su dau alhakin kai harin ba amma da alamu sun tabbatar a jiya Talata cewa suna kan hanyarsu ta zuwa garin Sake da ke kusa da Goma. Gwamnatin Congo da kwararrun Majalisar Dinkin Duniya sun ce kungiyar ta M23 na samun tallafin soji ne daga Rwanda, ko da yake kasar ta musanta hakan.

Kakakin kungiyar Lawrence Kanyuka a wata sanarwa da ya fitar ya ce, "M23 na zuwa ne domin kwato su da kuma kare su daga wadannan manyan hare-haren bindigogi," in ji kakakin, yayin da yake magana kan yakin da suke yi da jami'an tsaron Congo.

Dubban mutane ne suka tsere daga gidajensu zuwa Goma a cikin 'yan kwanakin nan, yayin da fadan ya tsananta, kuma asibitocin birnin na cike da fararen hula da suka jikkata, wadanda yawancinsu ke samun karancin kulawar lafiya.

Congo
Congo

Sama da mutane miliyan daya rikicin ya raba da muhallansu tun a watan Nuwamba da ta gabata, in ji kungiyar agaji ta Mercy Corps a ranar Talata. Hakan ya hada da miliyan 6.9 da suka rigaya suka tsere daga gidajensu a daya daga cikin manyan matsalolin jin kai da aka taba samu a duniya.

Kungiyar ta yi gargadin cewa, an kuma toshe manyan hanyoyin da ke kewayen Goma sakamakon harbe-harbe da karar bindigogi. Emilie Vonck, darektan kungiyar Mercy Corps a Congo ta ce "Hukumomin agaji yanzu suna kokawa da yanke shawara na yau da kullum akan neman lokacin mafi kwanciyar hankali don ba da taimako a cikin rahotannin da ke cewa ma'aikatan agaji sun shiga cikin tashin hankali."

Congo
Congo

A kan gadonta na asibiti a Goma, Feza Bongongwa, wata mata mai juna biyu da ta raunata a makon jiya a daya daga cikin hare-haren, ta roki a kawo karshen rikicin.

"Abu mafi mahimmanci shine a taimaka mana a kawo karshen wannan yakin," in ji Bongongwa. "M23 na samu cikin wahala."

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG