'Yan Senegal Mazauna Nijer Sun Yaba Da Matakin Shugaba Macky Sall

shugaban kasar Senegal Macky Sall

‘Yan kasar Senegal mazauna jamhuriyar Nijer sun bayyana farin ciki bayan da shugaba Macky Sall ya sanar cewa ba zai yi tazarce ba a zaben da za a yi a watan fabrerun 2024 koda yake a cewarsu lamarin na bukatar taka-tsan-tsan.

A shekarar 2021 gwamnatin Senegal ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska lamarin da ya sa ‘yan hamayya suka kaddamar da yaki da abinda suka kira yunkurin tazarcen shugaba Sall.

A jawabin da ya yi ta kafar television mallakar gwamnati a yammacin jiya litinin Macky Sally ya bayyana cewa ba zai shiga zaben shugaban kasa na faberun 2024 ba duk da cewa kundin tsarin mulkin Senegal bai hana masa shiga wannan fafatawa ba inji shi.

Shugaba Macky Sall wanda ke gab da kammala wa’adin mulkinsa na 2 na karshe ya aiwatar da gyaran fuska wa kundin tsarin mulki a shekarar 2021 abinda ke nufin daga yanzu shugaban kasa zai yi mulkin tsawon shekaru 7 sau 1 tak a maimakon shekaru 5 sau 2 matakin da ya haifar da dambarwa hade da kazamar tazoma domin a tunanin ‘yan hamayya take take ne irin na yunkurin tazarce kamar yadda ‘yan magana ke cewa sane sanin hauka zubda miyau.

Saurari rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Senegal Mazauna Nijer Sun Yaba Da Matakin Shugaba Macky Sall