Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Rikici A Senegal Yayi Sanadin Mutuwar Mutane 9 Bayan Da Aka Yanke Wa Wani Madugun 'Yan Adawa Hukunci  


Zanga-zanga a Senegal
Zanga-zanga a Senegal

An kashe mutane tara a wata arangama da ta faru a kasar Senegal ranar Alhamis, bayan da zanga-zanga ta barke sakamakon yanke wa madugun 'yan adawa Ousmane Sonko hukuncin dauri da aka yi. 

Ministan cikin gidan kasar Antoine Diome ya fada ta talabijin na kasar cewa, "muna Allah wadai da tashin hankalin da aka yi wanda ya kai ga lalata dukiyoyin gwamnati da na jama'a da kuma kisan mutane tara, a Dakar da Ziguinchor."

A jiya Alhamis, wata kotu a Senegal ta tabbatar da dukkan laifuffukan fyade da ake tuhumar Sonko da su, amma ta yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari bisa laifin gurbata matasa, tare da haramta mashi tsaya wa takarar shugaban kasa a shekarar 2024.

Zanga-zanga a Senegal
Zanga-zanga a Senegal

Sonko mai shekaru 48, shugaban jam’iyyar PASTEF-Patriots, ya dage kan cewa tuhume-tuhumen da ake masa na da nasaba da siyasa tun lokacin da aka fara gabatar da su a shekarar 2021, kuma bai halarci zaman kotun na ranar Alhamis ba.

An dai zarge shi ne da yi wa wata ma’aikaciyar shagon tausa fyade a shekarar 2021, da kuma yi mata barazanar kisa.

Ousmane Sonko
Ousmane Sonko

Lauyoyin Sonko sun shaida wa manema labarai a wajen kotun a jiya Alhamis cewa an yi masa wannan hukuncin ne domin hana shi takara da shugaban kasar Macky Sall a 2024. Babu tabbas dai ko Sonko zai iya daukaka kara kan hukuncin.

Sonko ya kasance mai sukar shugaban Senegal na yanzu kuma ana kallonsa a matsayin abokin hamayyar Sall da zasu fafata sosai a zabe mai zuwa.

Shugan kasasr Senegal Macky Sall
Shugan kasasr Senegal Macky Sall

A farkon makon nan, Sonko, wanda ke da farin jini ga matasan Senegal, ya yi kira da a gudanar da zanga-zanga a matsayin mayar da martani kan tuhume-tuhumen da aka yi masa. Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa an gudanar da zanga-zanga tare da sanya wuta akan tituna a Dakar babban birnin kasar.

Kamfanin yada labaran na Faransa ya kuma bayar da rahoton cewa jami’an tsaro sun harba barkonon tsohuwa kan ‘yan jarida da ke a kusa da gidan Sonko. A shafinsa na yanar gizo, AFP ya wallafa wani bidiyo da ya nuna wani dan jarida da masu daukar hoto da ke gujewa hayakin barkonon tsohuwa.

XS
SM
MD
LG