Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AU Ta Nuna Damuwa Kan Batun Nunawa ‘Yan Afirka Wariya Yayin Da Suke Kokarin Tserewa Daga Ukraine


France Africa
France Africa

Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta fada jiya litinin cewa, ta damu matuka da rahotannin da ke cewa an hana 'yan Afirka da ke zama a Ukraine 'yancin ketare iyaka yayin da suke kokarin tserewa rikicin Ukraine.

"Ba mu amince da rahotanni da ke nuna cewa ana nuna wa 'yan Afirka wariya ba, wannan zai zama abin ban mamaki na wariyar launin fata da kuma keta dokokin kasa da kasa," in ji shugaban AU, shugaban kasar Senegal Macky Sall, da shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka wallafa ta shafin Twitter.

Sanarwar ta kara da cewa, dukkan mutane na da 'yancin ketara iyakokin kasa da kasa a lokacin da ake rikici, kuma ya kamata su sami damar tserewa daga rikicin Ukraine, ba tare da la'akari da asalin kasarsu ko launin fata ba.

Tun da hare-haren y afara, dubban 'yan kasashen Afirka da wasu 'yan kasashen waje, musamman dalibai ne, suka yi ta tururuwa don barin kasar Ukraine, sakamakon hare-haren da Rasha ta yi.

To sai dai yayin da dubban daruruwan mutane ke yin tururuwa zuwa kan iyakokin kasar Ukraine, rahotanni sun bayyana cewa ana nuna wa 'yan Afirka wariya, har ya kai ga hana su ficewa daga Ukraine.

Mutane da dama sun yi musayar bidiyo da sakoni a kafafen sada zumunta, inda suka yi Allah wadai da wariya a tashoshin jirgin kasa da kan iyakokin kasar.

Ya zuwa yanzu dai ba a tantance gaskiyar bidiyon ba a cewar Kamfanin dillancin labaran Reuters.

~REUTERS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG