Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Senegal Ya Killace Kansa


Shugaban kasar Senegal, Macky Sall
Shugaban kasar Senegal, Macky Sall

Shugaban Senegal Macky Sall ya killace kansa, a matsayin kandagarki, bayan da yayi mu’amala da wani da aka gano yana dauke da kwayar cutar COVID-19.

Wata sanarwar da ofishin shugaban ya fitar da maraicen jiya Laraba, ta ce, duk da cewa sakamakon gwajin Sall, ya nuna baya dauke da cutar, bisa shawarar likitoci, zai killace kansa na tsawon kwanaki 15.

Yadda ake yi wa 'yan gudun hijira gwajin Covid 19 a Senegal
Yadda ake yi wa 'yan gudun hijira gwajin Covid 19 a Senegal

Haka nan, wata lauya a Senegal, Yeya Diallo, wacce ta bayyana a jiya Laraba cewa sakamakon gwajinta ya nuna tana dauke da cutar, ta bukaci jamma’a da su dau matakai kamar irinsu bayar da tazara domin gudun kamuwa da cutar da kuma yada ta.

Ya zuwa yanzu, Senegal ta bayyana cewa mutum 6,100 ne suka kamu da cutar, kana 93 kuma su ka mutu sakamakon kamuwa da cutar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG