Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SENEGAL: Gwamnatin Senegal Ta Katse Hanyar Sadawar Intanet Yayin Tashe-tashen Hankula Da Su Ka Barke a Kasar


FILE - Senegalese Gendarmerie block a road after protests burned tires and blocked roads in Dakar, June 3, 2023.
FILE - Senegalese Gendarmerie block a road after protests burned tires and blocked roads in Dakar, June 3, 2023.

Gwamnatin Senegal ta katse hanyoyin sadarwar intanet na wayar salula a wasu yankuna saboda tarzomar da ta yi sanadin mutuwar mutane inda aka rika yada sakonnin kiyayya da na son zuciya a yanar gizo, in ji sanarwar a ranar Lahadi.

A kasar da ke yammacin Afirka an shafe kwanaki uku ana kazamin zanga-zanga inda mutane 16 suka mutu. Wannan dai na daya daga cikin tashe tashen hankula mafiya muni da kasar ta gani a cikin shekaru da dama da suka gabata.

A makon da ya gabata, gwamnati ta takaita damar yin amfani da wasu dandalin aika saƙwanni, amma da yawa sun sami damar zagaya katsewar ta hanyar amfani da cibiyoyin sadarwa masu zaman kansu da ke sakaye sunan mai amfani da su.

Zanga-zanga a Senegal
Zanga-zanga a Senegal

Ba a fayyace yankunan da abin ya shafa ko kuma lokaci da za a takaita ba, amma manema labarai biyar na Reuters a fadin Dakar ba su iya shiga Intanet ta hanyar sadarwar wifi ba a ranar Lahadi da yamma, lokacin da zanga-zangar ta fara kankama.

"Saboda yawan yada sakonnin nuna kiyayya da kuma batanci da ake ta yi, an dakatar da Intanet na wayar hannu na wani dan lokaci a wasu sa'o'i," in ji sanarwar.

Abin da ya haddasa tarzomar shi ne hukuncin da aka yanke a ranar Alhamis din nan ma sanannen jagoran ‘yan adawar kasar, Ousmane Sonko, kan wata shari'ar fyade da ta shafe shekaru biyu ana yi. Magoya bayansa sun ce shigar da karar na da alaka da siyasa kuma shi kan shi ya musanta aikata wani laifi.

A ranar Alhamis, an wanke shi daga laifin fyade amma aka same shi da laifin bata tarbiyyar wata matashiya kuma aka yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari. Wannan hukuncin zai iya hana shi tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairu kuma masu zanga-zangar sun amsa kiran da ya yi na kalubalantar hukumomi.

Masu zanga-zangar sun kuma fusata saboda kin amincewa da shugaba Macky Sall ya yi ya yanke shawarar ba zai tsaya takara a karo na uku ba. Senegal ta iyakance wa'adi biyu ga shugaban kasa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG