'Yan Sandan Afirka ta Kudu Sun Kama Mutumin Da Ya Bada Shaidar Tayar Da Gobarar Da Ta Kashe Mutane 76

Gobarar ta garin Johannesburg a Afirka ta Kudu

An kama wani mutum ranar Talata, kuma zai fuskanci tuhume-tuhume 76 na kisan kai bayan ya bada shaida a bincike cewa shi ya tayar da mummunar gobara a Afirka ta Kudu a bara a lokacin da yake kokarin kawar da gawar wani da ya shake, ya kashe a harabar gidan bisa umarnin wani dillalin miyagun kwayoyi

WASHINGTON, D. C. - Amsa laifin mai ban mamaki ya zo ne a lokacin da mutumin ke ba da shaida a wani bincike na jama'a game da musabbabin gobarar da ta tashi da daddare a garin Johannesburg a cikin watan Agusta, wadda ta kasance daya daga cikin bala'o'i mafi muni a Afirka ta Kudu da ta yi sanadin mutuwar mutane 76.

Mutumin mai shekaru 29, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya ce ya kashe wani mutum ne a cikin ginin da ya lalace a daren da gobarar ta tashi ta hanyar lakada masa duka tare da shake shi, kamar yadda kafafen yada labarai na Afirka ta Kudu suka ruwaito na shaidar. Ya ce sai ya zuba man fetur a jikin mutumin sannan ya kyasta ashana ya cinna masa wuta.

Johannesburg, Afirka ta Kudu, Sept. 3, 2023.

Ya shaida cewa shi mai shan miyagun kwayoyi ne kuma wani dillalin miyagun kwayoyi ‘dan kasar Tanzaniya da ke zaune a ginin ne ya ce ya kashe mutumin.

Sa'o'i kadan bayan haka, 'yan sanda sun ce sun kama mutumin bayan shaidar da ya bayar. Har ila yau yana fuskantar tuhume-tuhume 120 na yunkurin kisan kai da kuma tuhumar kone-kone, in ji wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar. ‘Yan sanda sun ce zai gurfana a gaban kotu a birnin Johannesburg nan ba da jimawa ba, ba tare da bayar da kwanan wata ba.

Binciken da ya ke ba da shaida, ba na shari'a ba ne shi ya sa ikirari nasa ya zo da cikakken mamaki. Ana gudanar da binciken ne domin duba ko menene ya haddasa gobarar da kuma rashin tsaro da ka iya janyo mutuwar mutane da dama, an nemi ya bada shaida ne domin yana zaune a ginin.

Kwamitin da ke kula da binciken ya ba da umarnin kada a bayyana shi bayan shaidarsa, kuma lauyan da ke jagorantar gabatar da shaidun ya ce ba za a iya amfani da ikirari nasa a kansa ba saboda wannan binciken ba na shari’a ba ne.

Gwamnatin birnin Johannesburg ne ta mallaki ginin, amma wasu suka yi kane-kane da ginin suka rika ba da hayar dakuna ga daruruwan talakawa da ke neman wurin zama. Yawancin mutanen da ke cikin ginin dai bakin haure ne da ake zargin suna Afirka ta Kudu ba bisa ka'ida ba.

Har ila yau, ya haifar da fushi a Afirka ta Kudu cewa da alama hukumomi ba su da ikon hana kwace irin wadannan gine-gine da ake yi ba bisa ka'ida ba.

'Yan sandan Afirka ta Kudu dai sun bude shari'ar aikata laifuka kwanaki bayan gobarar watanni biyar da suka gabata amma ba a kama kowa ba sai jiya Talata.

Domin karin bayani - https://www.voahausa.com/a/wata-gobara-a-birnin-johannesburg-ta-kashe-akalla-mutane-73/7248869.html

-AP