Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 16 Sun Mutu, Wasu Da Dama Sun Jikkata A Harin Da Rasha Ta Kai A Gabashin Ukraine - Jami’ai


Rasha Ta Kai Wani Sabon Hari Da Ya Kashe Mutane 16 A Ukraine.
Rasha Ta Kai Wani Sabon Hari Da Ya Kashe Mutane 16 A Ukraine.

Akalla mutum 16 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata a ranar Laraba, bayan da Rasha ta yi luguden wuta kan wata kasuwa a wani birni a gabashin Ukraine, in ji jami'ai.

WASHINGTON, D.C. - Mummunan harin dai ya zo ne a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai ziyara Kyiv kuma ana sa ran zai sanar da ba da tallafin sama da dalar Amurka biliyan daya a matsayin gudunmawa.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Ya Kai Ziyara Ukraine
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Ya Kai Ziyara Ukraine

Kamfanin Dillancin Labaran Associated Press ya ruwaito cewa ya ga gawarwakin da aka rufe a kasa da kuma jami'an agajin gaggawa na kashe gobara a rumfunan kasuwar a Kostiantynivka da aka kai harin.

Firai Minista Denys Shmyhal ya ce an kashe akalla mutum 16, inda akalla mutane 28 ne suka samu raunuka, a cewar ministan cikin gida, Ihor Klymenko.

Ma’aikatan Agaji Na Tonan Wadanda Suka Makale A Baraguzo, Ukraine
Ma’aikatan Agaji Na Tonan Wadanda Suka Makale A Baraguzo, Ukraine

Ma’aikatan ba da agajin gaggawa sun kashe gobarar da ta lalata rumfuna kusan 30 a kasuwar da ke baje a waje, in ji Klymenko.

Ma’aikatan sun kuma yi ta binciken baraguzan ginin domin gano duk wani farar hula da ya makale.

Blinken na ziyarar ne don auna hare-haren ramuwar gayya na tsawon wata uku da Ukraine ta kwashe tana yi tare da ci gaba da nuna goyon baya ga hukumomin na Kyiv.

UKRAINE: Ma’aikata Na Kashe Gobara
UKRAINE: Ma’aikata Na Kashe Gobara

Hakan na faruwa ne yayin da wasu kasashen yammacin suke nuna damuwa kan yadda Ukraine ke jan kafa wajen fatattakar sojojin Rasha bayan wata 18 da aka kwashe ana yaki a cewar jami’an Amurka.

"Muna so mu tabbatar da cewa Ukraine tana da abin da take bukata, ba wai kawai don samun nasara a cikin hare-haren ba amma ya zamana suna da kayan yaki.

“Mun kuma kuduri aniyar ci gaba da yin aiki tare da abokan aikinmu yayin da suke sake gina tattalin arziki, da dimokiradiyya mai karfi.” Blinken ya ce.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG