WASHINGTON, D.C. - Wasu daga cikin mutanen da ke zaune a cikin tantuna da wasu tsare-tsare da ke cikin ginin, sun yi ta fadawa ta tagogi don guje wa gobarar da watakila ta hanyar haka ne suka mutu a lokacin, in ji wani jami’in karamar hukumar. Bakwai daga cikin wadanda gobarar ta rutsa da su yara ne, mafi kankanta cikinsu dan shekara 1, a cewar mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa.
Mutane kusan 200 ne ke zama a cikin ginin, in ji shaidun gani da ido.
Wani ganau ya ce ya ga mutane suna jefa jarirai daga ginin da ke konewa a kokarin ceto su kuma akalla mutum daya ya mutu a lokacin da ya yi tsalle daga wata tagar da ke hawa na uku inda kansa ya bugi kan titin siminti.
Hukumomin birnin sun ce iyalai 141 ne bala’in ya shafa amma ba za su iya tantance adadin mutanen da ke cikin ginin a lokacin da gobarar ta tashi ba. Amma yawancin mutanen da ke ciki 'yan kasashen waje ne, in ji jami'ai.
Ma'aikatan gaggawa suna sa ran samun karin wadanda abin ya shafa yayin da suke zagaya cikin ginin. An jera gawarwakin mutane da dama a gefen titin da ke kusa, wasu a cikin jakunkunan gawa, wasu kuma an lullube su da likkafanin azurfa da barguna.
Wasu mutane 55 kuma sun jikkata sakamakon gobarar da ta tashi da misalin karfe 1 na safe a tsakiyar cibiyar kasuwanci ta birnin Johannesburg, in ji kakakin hukumar agajin gaggawa ta Johannesburg Robert Mulaudzi.
“Wannan abin mummunan bala'i ne ga Johannesburg. Sama da shekaru 20 a hidimar aiki na, ban taba ganin irin wannan bali’in ba, ”in ji Mulaudzi.
-AP
Dandalin Mu Tattauna