'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Kisan 'Yan Bindiga Da Dama A Zamfara

Rundunar 'yan sanda

A wani lamari mai ban mamaki, 'yan bindiga da dama sun gamu da ajalinsu a lokacin da suka yi yunkurin kai hari a garin Matuzgi da ke karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara.

Yunkurin da 'yan ta'addan suka yi na kai hari a Garin ya samu cikas ne saboda jajircewar mazauna garin, inda suka yi wa maharan kwanton bauna sannan suka fafata a tsakanin su har suka yi wa 'yan bindigan mumunar ta'adi suka kuma kashe da dama daga cikin su.

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da samun gawarwakin 'yan bindigan guda takwas a hukumance, ko da yake majiyoyin cikin gida na nuni da cewa adadin ya zarta haka.

A cewar ASP Yazid Abubakar, kakakin rundunar 'yan sandan, "za mu iya tabbatar da kashe 'yan bindiga takwas ya zuwa yanzu, duk da cewa mun yi imanin za a samu karin adadin 'yan bindigan da aka kashe yayin da muke ci gaba da bincike a cikin daji."

Mazauna Matuzgi, wadanda suka jajirce har suka yi nasarar da suka samu, sun ba da labarin yadda suka tsaya-tsayin daka kan 'yan bindigan da ke dauke da muggan makamai.

Sun so su riske mu ne da nufin su kashe mu, amma Allah ya ba mu nasara,in ji wani mazauni yankin.

Yayin da 'yan fashin dajin ke ja da baya, shaidu sun bayyana cewa, sun kwashe gawarwakin 'yan uwansu akalla 12 da suka mutu, inda da yawa daga cikinsu ba a gansu ba.

Wasu karin rahotanni daga kauyen Magamin Diddi na karamar hukumar Maradun da ke makwabtaka da su sun nuna cewa an kashe wasu 'yan bindiga 10 a kauyen lokacin da suke kokarin tserewa daga Matuzgi, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu ya kai 35.

'Yan bindigan, wadanda ake kyautata zaton yaran kasurgumin 'dan taaddan nan ne, Kachalla Jummo Smally, wanda ke da Dabar SA a bayan dam na Bakalori aka fi sani da bayan ruwa.

Yayin da 'yan fashin ke ci gaba da addabar yankin, kauyuka da dama sun dauki makamai domin kare kansu, tare da yin taka-tsan-tsan game da jinkirin mayar da martani daga hukumomi.

Duk da wannan nasara da aka samu, al'ummar sun yi alhinin rashin nasu mutanen uku.

Jama'ar kauyukan na ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana, inda suke zaton ko 'yan bindigan na sake shirye-shiryen kai musu harin ramuwar gayya.

Mun samu labarin cewa 'yan bindigan na iya kokarin dawowa domin kwato gawarwakin mutanen su in ji Malam Bello, wani mazaunin garin.

Wannan rikici na baya-bayan nan dai ya nuna yadda tashe-tashen hankula ke kara kamari a jihar Zamfara, inda alummomi irinsu Matuzgi suka mike domin kare kan su, sakamakon tabarbarewar sha'anin tsaro a Jihar.

Yanzu haka dai a jihar Zamfara manoma da dama sun kasa zuwa gonakin su domin yin girbin gero da masara da duba sauran shukar da sukayi.

-Abdulrazak Bello