Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Sun Yi Gargadi Kan Shirin Gudanar Da Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa A Zamfara


'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)
'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Dalijan, ne yayi wannan gargadi yayin ganawa da shugabannin addinai da mambobin hadaddiyar kungiyar kwadago da kungiyoyin dalibai da sauransu.

Rundunar ‘yan sandan Zamfara ta gargadi mazuna jihar game da shiga zanga-zangar gama-garin da matasa ke shirin gudanarwa ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa akan manufofin gwamnatin tarayya.

Yayi ikrarin cewa ‘yan bindiga da ‘yan tada kayar bayan Boko Haram da sauran batagari zasu shiga cikin zanga-zangar kuma hakan ba zai haifarwa Najeriya da mai ido ba.

An ruwaito kwamishinan ‘yan sandan na cewa, “idan aka samu hatsaniya, ku za ta fi shafa fiye da kowa, ku kuke da abinda zaku rasa idan rikici ya zo.”

Ya cigaba da cewa, “galibin wadanda ke kiran da ayi zanga-zangar masu laifi ne da ‘yan bindiga da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da ‘yan fashi da makami da matasa zauna gari banza dake son suyi amfani da damar wajen fasa shagunan mutane suyi musu sata. idan mu a Zamfara muka shiga zanga-zangar, zamu kara tabarbara halin da muke ciki.”

A cewar hukumomin ‘yan sandan, gwamnatin tarayya bata da hannu a bala’in yunwar da al’umma ke fama da shi, illa ‘yan bindigar da suka hana manoma noma gonakinsu.

Sai dai, matsayar ‘yan sandan akan zanga-zangar bai yiwa mambobin hadaddiyar kungiyar kwadago da sauran masu ruwa da tsaki a ganawar dadi ba

Sun bukaci gwamnatin tarayyar ta sauke nauyin daya rataya a wuyanta, tare da saukaka rayuwa ga talaka wanda wannan shine dalili daya tilo na shirya zanga-zangar

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG