A jiya Alhamis, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya rattaba hannu akan dokar takaita zirga-zirgar babura a jihar.
Gwamnan ya sanya hannu akan dokar ne a fadarsa dake Gusau, babban birnin jihar.
Mai magana da yawun gwamnan, Suleiman Bala Idris, ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a jiya Alhamis, inda yace majalisar tsaron jihar ta yanke shawarar takaita zirga-zirgar baburan ne a yayin wani taron gaggawa daya gudana a Larabar data gabata.
An ruwaito sanarwar na cewa, “yau, gwamna Dauda Lawal ya rattaba hannu akan dokar dake takaitawa ko haramta zirga-zirgar babura daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safiya a koina a fadin jihar.
“Hakan wani yunkuri ne na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da dakile kalubalen tsaro da fadada matakan da gwamnati ke dauka wajen yaki da matsalar ‘yan bindiga da sauran nau’ukan laifuffuka a jihar.
“An baiwa antoni janar na jihar zamfara ikon gurfanar da duk wanda ya sabawa dokar a gaban kuliya.”
Dandalin Mu Tattauna