WASHINGTON, D. C. - Wani shaida ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun dira kasuwar ne da misalin karfe 11 na safiyar Lahadi inda suka bude wuta kan ‘yan kasuwar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar harin ga gidan talabijin na Channels ta wayar tarho.
Abubakar ya ce kawo yanzu ba a tantance adadin wadanda suka mutu a harin ba.
Kakakin ya kara da cewa an tura jami’an hadin gwiwa na sojoji da ‘yan sanda zuwa wajen da lamarin ya faru domin tunkarar ‘yan bindigar kuma yanzu an dawo da zaman lafiya a yankin.
“Eh, an samu wani lamari da safiyar yau (Lahadi) a Tsafe, ‘yan bindigar sun shiga garin, an kuma samu asarar rayuka, amma ba zan iya tabbatar da alkaluman ba yanzu. Har yanzu ina jiran DPO na Tsafe ya bayar da cikakken rahoton halin da ake ciki amma abin da zan iya tabbatar muku a yanzu shi ne sojoji da ‘yan sanda sun yi artabu da ‘yan ta’addan kuma an samu kwanciyar hankali a yankin yanzu.”
Wani mazaunin garin Tsafe Abubakar Tsafe ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa akalla mutane uku ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
‘Yan bindigan sun shiga ne da misalin karfe 11 na safe, suka fara harbin mutane ba kakkautawa a kasuwar, DPO na Tsafe ya tara jami’ansa da ke bakin aiki suka kulle ofishin ‘yan sanda, inda suka hana mutane shiga masu neman wurin samun mafaka.
Mazauna yankin sun kuma tabbatar da cewa dakarun Operation Hadarin Daji da aka tura garin Tsafe sun yi artabu da ‘yan bindigan a wani karo da ya tilasta musu gudu da komawa daji.
Dandalin Mu Tattauna