Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 25 A Wasu Kauyuka A Arewa Maso Yammacin Najeriya


'Yan bindiga a yankin jihar Kebbi
'Yan bindiga a yankin jihar Kebbi

Wasu ‘yan bindiga daga kungiyoyin miyagu sun kashe mutane 25 a lokacin da suka kai farmaki a wasu kauyuka hudu a yankin arewa maso yammacin Najeriya, a matsayin ramuwar gayya saboda farmakin da sojoji suka kai maboyarsu, a cewar wani jami’in tsaro a yankin.

A Katsina aka kai hare-haren a ranar Alhamis, jihar da ke daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga masu yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

‘Yan bindiga sun afka kauyukan Unguwar Sarki, Gangara, Tafi da Kore a karamar hukumar Sabuwa da yammacin ranar Alhamis, inda suka bude wuta kan mazauna kauyukan, a cewar Nasiru Babangida, kwamishinan tsaro na jihar Katsina.

Mazauna yankin da dama sun jikkata yayin da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su, a cewar Babangida.

Yawancin garuruwa a yankin arewa maso yammacin Najeriya sun kafa rundunonin mayakan sa-kai ko ‘yan banga domin yakar ‘yan bindiga a yankunan karkara da babu jami’an tsaro sosai, kuma bangarorin biyu na fafatawa sosai.

Yan Bindiga
Yan Bindiga

A baya-baya nan ‘yan bindigar sun kai farmaki a kauyukan ne a matsayin ramuwar gayya saboda hare-hare ta sama da sojojin Najeriya suka kai sansanoninsu a yankin da kuma a makwabciyar jihar Kaduna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da ‘yan bindigar 200, inji Babangida.

Kungiyoyin da suka boye a dazuzzukan jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna da Neja, sun yi kaurin suna wajen sace dalibai da yawa a makarantu a shekarun baya-baya nan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG