Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Garkuwa Da Mutane 150 A Zamfara Na Son Tattaunawa Maimakon Kudin Fansa


Yan bindiga
Yan bindiga

Wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da mutane 105 a yankin Arewa maso yammacin Najeriya a makon da ya gabata, ba kudin fansa su ke so ba, tattaunawa su ke so da gwamnatin jihar Zamfara, kamar yadda wasu iyalai biyar suka shaida bayan da ‘yan bindigar suka tuntube su a ranar Litinin.

WASHINGTON, D. C. - Gungun ‘yan bindiga na ci gaba da addabar Arewacin Najeriya, suna garkuwa da mutanen kauyuka da dalibai da masu ababen hawa domin neman kudin fansa.

‘Yan bindigar sun kai hari kauyukan Gora, Madomawa da Jambuzu da ke karamar hukumar Birnin-Magaji ta Zamfara a ranar Juma’a da daddare, inda suka yi awon gaba da mutane da dama.

Bello Mohammed, wani wanda matarsa da ‘ya’yansa uku da kuma kaninsa matashi na daga cikin wadanda aka dauko daga Gora, ya ce a daren ranar Asabar ne ya samu kiran waya daga ‘yan bindigar, da suka ce su ne suka kai harin.

"Ba sa bukatar wani kudin fansa daga gare mu, amma sun ce idan muna bukatar a dawo mana da 'yan uwanmu , sun ce mu da sauran jama'a mu isar da sako ga gwamnan jihar, cewa gwamnati ta neme su domin tattaunawa," abin da ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho kenan.

Masu garkuwa da mutanen ba su bayyana yanayin tattaunawar da suke so ba amma iyalai da dama sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun samu kira da sakon ta waya.

Ya ce an sace ‘ya’yan Wadatau Adamu guda hudu, ya kara da cewa hare-haren ‘yan bindiga sun sha faruwa a kauyukan da ke karkara da lunguna kamar Gora, inda ko kadan babu jami’an tsaro.

“Mun mika sakonsu ga shugabanninmu, muna jiran mu ga ko wani mataki za a dauka,” inji shi. Wasu mazauna garin uku sun ce suma sun samu irin wannan kiran.

Ba a dai samu jin ta bakin Kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara Mannir Kaura ba. Sai dai a wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 11 ga watan Mayu, Kaura ya soki wasu da ba a bayyana sunayensu ba da ya ce suna kokarin sai lallai an tattauna da kungiyoyi masu garkuwa da mutane.

Ya ce gwamnatin jihar Zamfara ta yi watsi da shirin samar da zaman lafiya da ‘yan bindiga wanda kungiyoyin wadannan mutane ke yi.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG