'Yan Damfara Sun Sauya Sabon Salo

Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a Najeriya, ta ce wasu ‘yan damfara sun samu lambar wayar mukaddashin hukumar, Ibrahim Magu, inda su ke amfani da lambar wayar domin damfarar jama’a.

Ra’ayin kwararru dai ya banbanta dangane da yuwuwar samar da lambar bogi daga wata lamba.

Samar da lamba ta hanyar yin amfani da wata lamba kamar yadda shafin bayanai na Wikipedia ya nuna, abu ne mai yiwuwa musamman a hanyuar sadarwa ta CDMA da ke ba da hanyoyin sadarwa masu yawa, amma kuma ba kasafai hakan ke faruwa a hanyar sadawar ta GSM ba

Hukumar ta EFCC dai ba ta fitar da cikakken bayani game da wannan almundahana ba, amma ta gargadi ‘Yan Najeriya da su zauna cikin shiri game da gungun ‘yan damfarar da suka saci lambar shugaban hukumar ta EFCC.

Sai dai hukumar ta ce a halin da ake ciki yanzu ‘yan damfarar suna kiran wasu na kusa da Magu inda su ke tambayar makudan kudade.