Hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, tayi barazanar dakatar da Najeriya, idan har ba’a hanzarta sasanta rikicin da ta kunno kai.
Hukumar ta yi barazanar ne a wani wasika da ta aikewa shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Amaju Pinnick, a jiya litinin.
FIFA, tace idan aka zartar da hukumcin da wata kotu ta yanke a Jos, zai kasance tafkar katsalandan ne ga harkokin hukumar kwallon kafa ta Najeriya, wanda hakan ya sabawa sashi na 15 da 17, na ka’idojin gudanarwa na hukumar kwallon kafa ta duniya, wace Najeriya ma wakiliyace.
Wannan sashi dai ya haramtawa wani ko kuma wata hukumar sa baki a harkokin cikin gida na hukumar kwallon kafa kuma wajibi ne ‘ya’yan hukumar su mutunta wannan.
Ita dai kotun ta zartar da hukumci cewa an rushe zaben Amaju Pinnick, kuma zata fara sauraron karar a ranar 30, ga watan Mayu, na wannan shekarar.