Kwallaye biyu da Jamie Vardy ya zura ne suka ba kulob dinsa na Leicaster City nasarar doke Sunderland a cikin gidan ta da ci biyu da daya a karshen mako, lamarin da yake dada kusantar da ita da lashe kofin gasar Premier ta bana, yanzu haka dai kungiyar na tabbacin karasa kakar wasanni ta bana a cikin kulob hudu na sama biyo bayan kashin da Totten ham ta ba Manchester da ci uku da nema.
Yanzu kungiyar Leicaster tana sama n teburin gasar Premier da maki 72, tare da tazarar maki bakwai tsakanin ta da kungiyar Totten Harm dake matsayin ta biyu da maki 65, Arsenal kuma ta yi kunnen doki da kungiyar West Ham da ci uku da uku ne a tebur da maki 59, yayin da Mancheter City ke fama da take ta hudu da maki 57, bayan da tayi galabar doke West Brom da ci biyu da daya, wannan kashin da Manchester ta sha yasa ta koma ta biyar da maki 53.
A can kasar Jamus kuma Bio Munich c eke kusantar daga kofin gasar Bundes legas karo na hudu a jere Kenan, bayan da karshen makon nan suka sake wanzar da tazarar maki takwas a sakamakon doke kungiyar Stud Guard da ci uku da daya, Bayern na bukatar maki gama sha daya ne a cikin wasannin ta biyar na karshe da suka rage domin ta sami lashe kofin ga kocin ta Pep Guardiola kafin komawar sa kungiyar Manchester City a gasar wasanni.
Ga cikakken rahoton Murtala Faruk.