Bincike da aka gudanar ya tabbatar da cewar idan ka yawaita cin “Albasa” tana taimakawa wajen kauce ma kamuwa da cututtuka da dama, wanda suka hada da cutar amosalin hanji "Colorectal Cancer" a turance da sankarar ciki "Stomach Cancer". Dr. Tunde Ajobo, na asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan, ya bayyanar da sakamakon binciken.
Yace Albasa tana dauke da wasu sinadarai da suke taimakama wasu kwayoyi a cikin jinin mutun, don bashi lafiya a lokacin da jini ke yawo a cikin jikin mutun. Yace idan mutun yana yawaita cin albasa, ruwan nata zai taimaka wajen yakar cuttuka da dama.
Haka ya bayyanar da albasa a cikin jinsin kayan da suke gina jiki da bama jiki wadatacciyar lafiya, kamar su ganyen Binida zugu, citta, albasa mai lawashi, da dai sauran su. Sai ya kara da cewar Albasa na kunshe da sinadarin bitamin C, ya kara da cewar an dade ana noman albasa, da sauran jinsin ta, wanda suke taimakawa ba kawai wajen kamshi ba a abinci, har ma da taimakawa wajen bada lafiya mai nagarta.