Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Kin Zartar Da Hukuncin Da Ya Dace Kan Masu Fyade


Matsalar fyade ta yi kamari a wasu sassan Najeriya irin su jahar Kano da kewaye, ta dalilin haka ne muka sami zantawa da wata mai rajin kare hakkin dan adam ta kungiyar Isa wali Initiatives Barista Amina Hanga, ta ce sakacin wasu mahukunta na rashin hukunta wadanda suka aikata laifin fyade na daga cikin abubuwan da ke kara ta’azara matsalolin fyade.

Ta kara da cewa jihar kano ta gabatar da wata doka a shekarar 2014 dangane da matsalolin fyade , amma har ka kawo yanzu matsalar ta ki ci taki cinyewa. A hirar su da wakiliyar dandalinvoa Baraka Bashir, ta kara da cewa ya zama wajibi a zaratar da hukuncin da ya dace idan ana so a kawo karshen matsalar.

A jawabin ta, Barrister Amina ta yi karin bayanin cewa wasu daga cikin wadanda suka aikata laifin kan bada cin hanci domin a sake su, kuma hakan nasa wadanda suke aikata wannan mummunan aiki ci gaba da aikata mugayen aiyukan su.

Daga karshe ta yi kira ga hukumomi da su ji tsoron Allah domin gudanar da aiyukan su kamar yadda doka ta tsara, domin hakan zai taimaka wajan gargadi da zama ishara ga masu irin wannan hali a duk inda suke.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG