Dr. Ibrahim Haliru Gwarzo, dan asalanin karamar hukumar Gwarzo ne dake jihar Kano a Najeriya. Ya samu damar karatun shi na Firamari da sakandare duk a jihar Kano, Sannan yaje jami'ar Maiduguri a jihar Bornon inda ya samu damakar kamala karatun shi na aikin likita. Kimanin shekaru 9 kenan da ya kammala karatun shi na aikin likita.
Bayan kamala karatun shi yayi aiki a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, dake birnin Kano a Najeriya, ya kuma yi aiki na dan takaitaccen lokaci a asibitin dake karamar hukumar Gumel a Jihar Jigawa, da asibitin cocin anglican a karamar hukumar Olokoro dake jihar Abia a kudan cin Najeriya, a lokacin aikin bautar kasa. Yanzu haka dai Dr. Ibrahim, yana karatun digiri na biyu a fannin kula da lafiyar alumma “Public Health” a turance, a Jami'ar Texas A & M dake jihar Texas a kasar Amurka, wanda yake sa ran cigaba har zuwa digirin digrgiri idan Allah yasa.
Dr. Ibrahim Gwarzo, yayi karin haske akan banbancin karatun kasar Amurka da na gida najeriya. Inda yake gani akwai matukar banbancin tsakanin yadda karatu yake a Najeriya, da kuma yadda yake a Amurka. Sai idan mutum yazo kasar Amurka, sannan zai fahimci irin banbancin. Kadan daga cikin abunda Dr. Ibrahim, ya lura da shi a kasar Amurka. A gida Najeriya, mafi yawan cin irin koyarwar da akeyi a makaratun gaba da sakandare, za aga ana dora wa dalibai nauyin sayen takaddu “handouts” domin su karanta su haddace, lokacin jarrabawa kuma suyi bayani ko a rubuce ko da baki abunda aka koya musu.