A yau Alhamis ne 'yan Burtaniya suka kada kuri'ar zaben 'yan majalisar dokokin kasar.
WASHINGTON, D. C. —


Miliyoyi masu kada kuri’a sun halarci rumfunan zabe inda ake sa ran za a zabi sabon Firaiminista.


Wasu zasu gabatar da katin zabensu na shaida kafin su kada kuri’a. Za a kuma rufe rumfunan da karfe 10 na dare agogon Najeriya inda a lokacin ne ake sa ran fara sakin sakamakon zaben.