Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rishi Sunak Ya Lashe Zaben Zama Sabon Firaministan Burtaniya


Sabon Firaminista Rishi Sunak
Sabon Firaminista Rishi Sunak

Rishi Sunak ya zama Firaminista na uku a Birtaniya a ranar Talata kuma a yanzu dole ne ya maida hankalinsa ga shawo kan matsalar tattalin arzikin da ta bar kasar cikin mawuyacin hali da kuma miliyoyin 'yan Birtaniyya da ke fafutukar samun kudin abinci da na makamashi.

Sunak, wanda ya zama shugaban Burtaniya mai launin fata na farko, ya gana a fadar Buckingham tare da Sarki Charles III, wanda ya amince da murabus din Liz Truss. A tsarin mulkin Biritaniya, sarkin yana taka rawa wajen nada shugabannin gwamnati.

Rishi Sunak tare the Sarki Charless III
Rishi Sunak tare the Sarki Charless III

Ana sa ran Sunak - dan shekaru 42 kuma shugaba mafi karancin shekaru a Biritaniya a cikin sama da shekaru 200, nan da nan zai fara nada majalisar ministoci tare da shawo kan tattalin arzikin da ke fuskantar koma baya.

Firaminista na uku na masu ra'ayin rikau a bana, zai kuma yi kokarin hada kan jam'iyya mai mulki da ke cike da rarrabuwar kawuna.

An zabi Sunak a matsayin shugaban jam'iyyar na masu ra'ayin mazan jiya mai mulki ranar Litinin yayin da take kokarin daidaita tattalin arzikinta, da kuma shahararsa, bayan dan gajeren koma bayan da ta samu a lokacin da Liz Truss ke mulki.

Lizz Truss
Lizz Truss

Truss ta yi murabus ne bayan ta ba da sanarwar bainin jama'a a kofar fadar gidan gwamnati da ke 10 Downing St, makonni bakwai bayan da marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu ta nada ta a matsayin Firayim Minista.

Manyan abubuwan da Sunak zai sanya a gaba su ne nada Ministoci, da kuma shirya sanarwar kasafin kudin da za ta bayyana yadda gwamnati ke shirin fitar da biliyoyin Fam (dala) don cike gibin kasafin kudi da aka samu sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da tattalin arzikin kasa, da kuma tabarbarewar ta.

Sunak ya zama Firaminista makonni kadan bayan ya sha kaye a hannun Truss a zaben masu ra'ayin mazan jiya don maye gurbin tsohon Firaminista Boris Johnson.

Truss ta amince a makon da ya gabata cewa ba za ta iya aiwatar da shirye-shiryenta ba - amma bayan yunkurin nata ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki a daidai lokacin da miliyoyin 'yan Birtaniyya suka rigaya su ke kokawa da hauhawar farashin rance da hauhawar makamashi da farashin abinci.

An zabi Sunak a matsayin shugaban masu ra'ayin mazan jiya ne bayan ya zama dan takara daya tilo da ya doke 100 daga 'yan majalisar wakilai don tsayawa takara a zaben jam'iyyar. Sunak ya doke abokin hamayyarsa Penny Mordaunt, da Johnson da aka hambarar, wanda ya dawo hutu daga kasar Caribbean don neman goyon baya na yunkurin dawowarsa amma ya kasa samun isashen goyon baya don yin takara.

~ AP

XS
SM
MD
LG