A yau Talata jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya a Burtaniya ta Conservative Pary, ta zabi Boris Johnson a matsayin sabon shugaban ta, wanda kuma a dalilin haka, zai zama sabon Firai Ministan kasar na gaba.
Shi dai Johnson ya kada abokin takarar shi ne Sakataren Harkokin wajen kasar Jeremy Hunt, bayan kammala kada kuri’u da akayi a daren jiya Litinin, da tazarar kashi 66 cikin 100 na kuri’un da aka jefa, yayinda shi kuwa Jeremy ya sami kashi 34 cikin 100 na kuri’un.
“Zamu hada kan wannan kasar, kuma zamu kaita mataki na gaba” a cewar Johnson, lokacin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar, jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben.
Ya kuma dau alwashin kawo karshen zaman Burtaniya cikin kungiyar kasashen Turai daga nan zuwa 31 ga watan Oktoba.
A gobe Laraba ne dai Johnson zai maye gurbin Theresa May a matsayin sabon Firai Ministan na Burtaniya.
Facebook Forum