Wannan muhimmin ci gaba ya biyo bayan kaddamar da rumbun taswirar bayanai da rajistar hukumar NiDCOM a Abuja a ranar 29 ga Yuni, 2021, da nufin tattara cikakkun bayanai masu inganci game da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje.
Bayanai da aka samu daga kafafen yada labaran cikin gida na Najeriya sun nuna cewa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje daga kasashe dabam daban har 28 ne suka yi rajista.
A karkashin alkaluman da NiDCOM ta bayar, kasar Burtaniya ce ke kan gaba da kashi 22.5 cikin 100 na ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da suka yi rajista. Daga na sai Amurka da ke bi a baya da kaso 21.4 cikin 100, sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa da ta zo ta uku da kashi 5.4.
Sauran wuraren da ‘yan Najeriya masu rajista suka yi fice sun hada da kasar Qatar mai kashi 4.8, Canada kashi 4.4, Afirka ta Kudu kashi 4.0, Jamus kashi 2.5, Saudi Arabia da Italiya kowanne da kashi 2.3, Ghana kashi 1.5, Malaysia kashi 1.1, sai Faransa kashi 0.9 bisa dari.
Hakazalika, bayanan sun kuma nuna cewa Australia na da kashi 0.7 bisa dari, China kashi 0.7 bisa dari, Jamhuriyar Benin kashi 0.7 bisa dari, Saliyo kashi 0.7 bisa dari, Turkiyya kashi 0.7 bisa dari, Switzerland kashi 0.7 bisa dari, Rasha kashi 0.6 bisa dari, Philippines kashi 0.6 bisa dari, Jamhuriyar Nijar kashi 0.6 bisa dari, Ireland kashi 0.6 bisa dari, Ukraine kashi 0.5, sai Kyrgyzstan mai kashi 0.1 cikin dari.
Yayin da wadannan alkaluman ke ba da haske game da yadda dandazon ‘yan Najeriya ke zaune a kasashen ketare, har yanzu lambobin rajista ba su da yawa.
Abdulrahman Terab, shugaban fasahar aika bayanai na NiDCOM ya yi karin haske kan wannan batu.
“Mafi yawan ‘yan kasashen waje suna samun kwarin gwiwa ne kawai a kasar, muna iya kokarinmu wajen karfafa gwiwar ‘yan kasashen waje su yi rajista ta yanar gizo, musamman a duk lokacin da muke da wasu shirye-shirye, ko abubuwan da suka faru ko ayyuka," a cewar Terab.
Bayanan da NiDCOM ta fitar sun nuna muhimmancin kiyaye sahihan bayanan al'ummar Najeriya, wadanda ba wai kawai suna taimakawa wajen karfafa alaka mai karfi da 'yan Najeriya a kasashen waje ba, suna kuma ba da haske ga masu tsara manufofi da hukumomin gwamnati.
Yayin da ake ci gaba da kokarin yin rajista da kuma samun kwarin gwiwa kan tsarin, hakikanin alkaluman ’yan Najeriya mazauna kasashen duniya da ake da su za su kara fitowa fili domin taimakawa gwamnati wajen inganta harkokin ci gaba na gida da waje a bangaren diflomasiyya, ci gaban ilimi da sauransu.
~Yusuf Aminu Yusuf
Dandalin Mu Tattauna