BOM YA TASHI SASSA UKKU A GARIN MAIDUGURI
Yau asaabar aka samu tashin bom a wurare ukku a cikin birnin Maiduguri, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma raunata wasu
Da musalin karfe 11 ne aka samu rahoton tashin bomb na farko a wani yanki na tashar Baga inda ake hada-hadar saye da sayarwa da kuma ake da cunkoson jamaa da dama.
Wannan tashin bomb na farko yasa mutane cikin wani halin kaka nikayi sakamakon irin barnan da wannan bomb din yayi wanda yayi musabbabin mutuwar mutane da dama wanda har yanzu ba a samu kiyasin adadin mutanen ba.
Awa daya da tashin wannan bomb din aka samu labarin tashin wani bomb din a daf da bakin kasuwar littinin, wanda kuma daga bisani muka sake samun labarin tashin wani bomb din a tashar Borno express, daya daga cikin manya-manyan tashoshin dake hada-hadan mutane daga wannan gari zuwa wancan gari. A cikin garin na maiduuri a wannan wurin ma ance an samu hasarar rayuka da kuma jikattan wasu.
Sai bayanai na cewa babban asibitin dake cikin garin Maidugurin suna da gawarwaki mutane 36wadan da mafi yawan su mata ne sailin nan da wasu majinyata da yawan su yakai 70 wadanda ake kyautata zaton cewa an kwaso su ne daga tashar Baga.
‘’Mutane 36 ne suka mutu wadanda kuma suka samu rauni su 73 ne wadanda ni da kaina na kirga’’
Sai wadanda ake kira Civilian JTF wato yan kato da gora sun tsananta binciken abin hawa a cikin garin na Maiduguri, wanda hakan ya kara cunkoson ababen hawa a cikin garin na Maiduguri.
‘’Irin matasan nan ma da yawa yan kato da gora da yawa akai akai……
Akace an rufe wasu hanyoyi ba shiga.
SaI wakilin sashen Hausa Haruna Dauda yace kwamishinan Sharaa Barista Kaka Shehu Lawal na jihar ya tabbatar da aukuwar wannan lamari kuma suna nan suna bi asibitoci suna bada umurni a yi wa wadannan mutanen magani kyauta gwamnati ce zata biya
Ga dai Haruna Dauda Biu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5